
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kama wata mata yar kunar bakin wake wacce ta yi yunkurin shiga birnin Maiduguri.
A wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter rundunar ta ce dakarunta na bataliya ta 251 sun tare yar kunar bakin wake a Gonikalachari.
“Sojojin Bataliya ta 251 dake Maiduguri sun kama wata mace yar kunar bakin wake wacce tayi kokarin shiga birnin Maiduguri ta tayar da bom din dake jikinta domin tayi barna kan yan Najeriya da basu ba su gani ba,” sakon ya ce.
Da aka yi mata tambayoyi yar kunar bakin waken mai shekaru 19 ta ce sunanta Shaidatu kuma ta fito ne daga Gwoza.
Kuma an turo ta ne ita kaɗai ta kai harin bayan da ta shafe shekaru 3 a Dajin Sambisa.