An Kama Wasu Mutane Biyu Suna Aikata Lalata A Cikin Coci A Maiduguri

Ƴan sanda a jihar Borno, sun kama wasu mutane biyu da aka samu suna yin zina a cikin cocin All Saint Protestant Church Police College dake Maiduguri.

Mutanen da aka kama sun haɗa da Kaka Ali Umar mazaunin titin Damboa da kuma Khadijah Adam dake Ngomari an kama su ne suna aikata laifin a ranar Litinin da misalin ƙarfe 11:40 na safe.

Rabaran Danjuma Adamu ya faɗawa ƴan sanda cewa suna tsaka da lalata da juna a cikin cocin sa lokacin da ya kama su.

Khadija ta ce Kaka Ali ya biya ta naira 1000 domin yayi lalata da ita sau ɗaya.

Mutanen na cigaba da fuskantar bincike a ofishin ƴan sanda na Metro dake Maiduguri.

More from this stream

Recomended