An kama wasu masu taimakawa ƴan fashin daji a Katsina

Rundunar Ƴan Sandan jihar Katsina ta kama wani mai suna, Aminu Hassan da ake zargi da taimakawa ayyukan ta’addanci a jihar.

Abubakar Sadiq mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar ya ce an kama Hassan ne lokacin da jami’an rundunar ke gudanar da sintiri akan hanyar Yantumaki- kankara

Da yake magana da ƴan jaridu a hedkwatar Sadiq ya ce an kama karin wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a aikata laifin da ake zargin Hassan.

Mai magana da yawun rundunar ya ce an kama mutanen ne da kakakin sojoji da za su je kai wa ƴan fashin daji.

Jihar Katsina dai na daga cikin jihohin dake fama da hare haren ƴan bindiga a yankin arewa maso yamma.

More from this stream

Recomended