Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji sun kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan bindiga ne a jihar Zamfara.
Daya daga cikin wadanda ake zargin, Aminu Ibrahim, an ce shugaban jam’iyyar PDP na gundumar Birnin Yero a karamar hukumar Shinkafi.
PRNigeria ta tattaro daga wata majiyar leken asiri ta soji a jihar cewa an kama Ibrahim, tare da abokan sa, wato Musa Usman Seun da Isah Mohammed a ranar Litinin.
Majiyar ta ci gaba da cewa: “Dakarun rundunar hadin gwiwa ta shiyyar Arewa maso Yamma Operation HADARIN DAJI da suke aiki da sahihan bayanan sirri kan ayyukan wani fitaccen dan bindiga da nufin fasa kwaurin makamai zuwa cikin jihar Zamfara, nan take sojojin suka tare hanyar tare da cafke wasu mutane 3 da ake zarginsu da aikatawa.
“Mutane 3 da ake zargin sun hada da Musa Usman Seun, Aminu Ibrahim, da Isah Mohammed an kama su ne kwanan nan a Shinkafi a ranar 22 ga watan Junairu 2024 kuma an kwato kudi naira miliyan biyu da dubu dari biyar da tamanin, Volkswagen Wagon 1, wayoyin hannu 3 da sauran kayayyaki.”