Mazauna yankin Nepa dake ƙaramar hukumar Jos North ta jihar Filato sun kama wani mutum da ake zargin mai garkuwa da mutane ne da ya karbi kuɗin fansa naira miliyan 1,500,000 daga wurin ƴan uwan wanda ya yi garkuwa da su a Jos babban birnin jihar.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar DSP Alabo Alfred wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wanda aka kama ɗin na tsare a sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane na rundunar inda yake amsa tambayoyi.
Wani ɗan bijilante dake unguwar ta Nepa da ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗawa jaridar Daily Trust a ranar Alhamis cewa bayan mazauna unguwar sun kama wanda ake zargin sai suka gaggauta miƙa shi hannun jami’an bijilante dake yankin.
Ya ƙara da cewa daga bisani sai aka kai shi ofishin ƴan sanda na Laranto.
Da yake zayyana yadda lamarin ya faru ɗan bijilanten ya ce “Mai garkuwar da mutanen ya sace wasu ƙananan yara biyu ɗaya mai shekaru huɗu ɗaya kuma mai shekaru biyar.Bayan da ya karɓi kuɗin fansa miliyan 1.5 sai yaƙi ya sake su nan take,”
Ya ƙara da cewa a lokacin da ya dawo duban yaran a kangon gidan da ya ajiye su ne sai kawai akaji kukan su abun da ya ankarar da mutanen yankin halin da ake ciki.
Ganin mutane ya sa mai garkuwar ya yi ƙoƙarin tserewa amma mutane suka kama shi tare da kuɗin.