Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata laifin fyade ga karamar yarinya.
Kakakin rundunar SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a ranar Talata.
Wadanda ake zargin sun hada da Hassan Nasir mai shekaru 25, Uzairu Dan Fulani mai shekaru 25 da kuma Yahaya Edward, 26.
Suleiman ya ce an kama wadanda ake zargin ne da laifin yi wa wata yarinya ‘yar shekara 15 fyade a karamar hukumar Mayo Belwa.
Ya kara da cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin mazauna Sabon Pegi ne, Ngurore, Yola ta Kudu, dayan kuma dan unguwar Gabasa Mayo Belwa ne a karamar hukumar Yola ta Kudu.