An kama wasu mutane biyu da ake zargi da neman yin auren jinsi a Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, kwamandan Hisba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar.
Ya kara da cewa an ga wasu samari guda biyu masu suna Khalifa da Abubakar a bidiyo suna kokarin sumbatar juna a wajen wani biki, wanda wata kila bikin aurensu ne.
Sai dai wadanda ake zargin sun musanta zargin cewa bikin ranar haihuwa ne maimakon bikin aure, kamar yadda aka yi ikirari.
Daya daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Khalifa, ya bayyana cewa shi ne ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa, kuma abokinsa Abubakar ya kawo masa biredi.
Mutanen biyu suna hannun hukumar Hisbah, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.