An kama mutane biyu a yayin da aka gano wurin ƙera bindigogi a Jos

Sojojin rundunar Operation Safe Haven dake aikin samar da tsaro a jihar Plateau sun bankaɗo tare da lalata wata masana’antar ƙera bindigogi dake Vom a karamar hukumar Jos South dake jihar.

A cewar wata sanarwa da aka fitar ranar Asabar, an bankaɗo masana’antar a farmakin da aka kai biyo bayan bayanan sirri da jami’an tsaro suka samu.

Sojojin sun gano bindigogi da dama da kuma injinan da ake amfani da su wajen kera bindigogi da ake rarraba su a jihohin daban-daban.

Bindigar AK-47 guda biyar aka gano a wurin, da bindigar mashingan da kuma bindiga kirar pistol da sauran sassan bindiga iri daban-daban.

Sanarwar ta kara da cewa an kama mutane biyu Michael Dung mai shekaru 33 da kuma Yusuf Pam mai shekaru 43 da ake zarginsu s da hannu wajen sayarwa tare da taimakawa bazuwar makamai.

More from this stream

Recomended