
Yan sanda sun kama wasu mata su hudu Nonye Osi, Akintan Adedayo, Elizabeth Bishop a Bukola Oladapo, da kuma wani namiji, Jimoh Bashiru bayan da aka same su da hada biki suka sayar da wani jariri dan sati biyu kan kudi naira miliyan 3 a jihar Lagos.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Hundeyin ya ce sashen binciken manyan laifuka na rundunar na tuhumar mutanen da laifukan yin garkuwa tare da sace yaro.
Ya ce a ranar 5 ga watan Mayu ne wani mutum ya shigar da kara ofishin yan sanda na Ajah cewa wani da ba’asan waye ba ya yiwa wata yar uwarsa Miss Happiness mai shekaru 16 ciki.
“Binciken da aka gudanar ya nuna cewa saboda rashin kudi ya sa mahaifiyar wanda ya shigar da korafin ta bawa wata mai suna Nonye Osi ta ajiye ta har ya zuwa lokacin da za ta haihu.
” Amma kuma Nonye ta hada baki da wasu ta sauyawa Happiness wurin zama da ba a sani ba. Bayan da aka gano ta ne aka same ta babu cikin kuma babu jariri,”
Biyo bayan bincike ne aka gano jariri a yankin Badagry dake Lagos kana aka kama mutanen hudu.