An Kama Mutane 2 Saboda Zargin Yanke Maƙogoron Maƙwabcinsu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta kama wasu mutane biyu Abdullateef Yakubu da Yakubu Olanrewaju na unguwar Shao Garage, Ilorin, bisa zargin su da yanka makogwaron wani makwabcinsu saboda ɗan rikici da ke tsakaninsu.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:00 na safiyar ranar Litinin a unguwar Shao Garage da ke Ilorin a karamar hukumar Ilorin ta Gabas a jihar Kwara.

Wata majiya da ke da masaniya kan lamarin ta shaida wa wakilinmu cewa, wani dan’uwan wanda abin ya shafa mai suna AbdulRazaq Babatunde, wanda ihun wani mazaunin garin ya ja hankalinsa, ya fito ya tarar da kaninsa Abubakar Babatunde a cikin jinin caɓa-caɓa.

Majiyar ta kara da cewa “Daga bisani an garzaya da shi asibitin koyarwa na Jami’ar Ilorin domin kula da lafiyarsa”.

More from this stream

Recomended