Rundunar ƴan sandan jihar Niger ta ce ɓata gari 11 aka kama da ake zargi suna da hannu a ƙone wani sashe na sakatariyar ƙaramar hukumar Tafa dake jihar..
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Wasiu Abiodun a cikin wata sanarwa ranar Alhamis ya ce an cinnawa motoci biyu wuta aka kuma farfasa wasu ya ƙara da cewa ɓata garin sun kuma saci wasu kayayyakin masu muhimmanci.
Ya ce an kai harin da misalin ƙarfe 09:30 na safe kuma wasu daga cikin maharan sun fito ne daga yankin na Tafa dake ƙaramar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna da kuma hayin Dikko dake ƙaramar hukumar Gurara ta jihar Niger
Ya ƙara da cewa wasu daga ɗauke da makamai.