An kama matashin da ya yi ƙaryar an sace masa al’aura

Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta cafke wani matashi mai suna Sunday Ebube Linus da laifin ƙaryar bacewar ƴaƴan marainansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Bright Edafe, yayin da yake tabbatar da kama Linus ya kuma gargadi jama’a game da ɗaukan doka a hannu a matsayin hanyar hukunta masu laifi.

Jami’in ya rubuta a shafinsa na X (wato Twitter) a ranar Laraba cewa “wanda ake zargin mai shekaru 18, Ebube Linus, a ranar Lahadi, 8 ga Oktoba 2023 a DBS Road Asaba, ya yi ƙaryar cewa wata tsohuwa a cikin a-daidaita-sahun ta taba shi kuma ƴaƴan marainansa (azzakarinsa) sun ɓace”.

Ya ƙara da cewa, “Sama da bata gari 100 ne suka taru suka ci wa wannan mata zarafi, suka tuɓe ta tsirara suka yi mata duka har ta kai ga kashe ta”.

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...