An kama matashin da ya ƙone wata har lahira saboda zargin maita a Bauchi

Wani matashi dan shekara 30 mai suna Hamza Umar, ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda a jihar Bauchi bayan da ya zuba wa wata yarinya kananzir da kone ta bisa zargin maita.

Wannan lamari dai an bayyana shi ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya fitar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce wanda ake zargin ya aikata laifin ne a lokacin da wanda ake zargin ta shiga gidansa da ke unguwar Rafin Albasa a cikin garin Bauchi babban birnin jihar, tana mai cewa babbar yayarta ce ta aiko ta domin ta kashe Hamzan.

“Wanda ake zargin ya ce ya yi yunkurin sa yarinyar ta bar gidansa, amma ya ce ta dage sai ta binne wasu laya a kusurwar gidan,” a cewar SP Wakili.

More from this stream

Recomended