Wani jami’in ɗan sanda mai suna Aminu Muhammad dake aiki da rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗa komar abokan aikinsa ƴan sanda kan zargin da ake masa na aikata fashi shi da makami da kuma satar mota.
Williams Ovye-Aya mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Kogi ya faɗawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa an kama ɗan sandan mai muƙamin insifecta kuma ana cigaba da gudanar da bincike.
Ya ce tuni kwamishinan ƴan sandan jihar, Bethrand Onuoha ya bayar da umarnin yin bincike domin gano yadda ɗan sanda yake da hannu a aikata laifin da ake tuhumarsa da aikatawa.
A cewar NAN an kama ɗan sandan ne akan wani fashi da makami da ake zargin anyi a cikin birnin na Lokoja.
Ɗan sandan ya ɗauki motar da aka yi fashinta inda ya kaiwa mai gyara domin a sauya mata kama ta yadda mai ita bazai gane anan ne kuma dubunsa ta cika bayan da wani da ya san motar ya ganta a wurin gyara ya kuma gaggawar sanar da jami’an tsaro.