
Ministan ma’adanai, Dele Alake ya ce an kama wasu ƴan kasar waje su uku dake haƙar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Rafin Gabas dake ƙaramar hukumar Kokona ta jihar Nasarawa.
A wata sanarwa da aka fitar, Segun Tomori mai taimakawa ministan kan kafafen yaɗa labarai ya ce jami’an tsaron na musamman na fannin ma’adinai sun rufe wurin haƙar ma’adinan dake samun kariyar wasu ɓatagarin jami’an tsaro.
Sanarwar ta jiwo ministan na cewa wannan wata gagarumar nasara ce a yakin da ake na haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a ƙasarnan inda ya ƙara da cewa ana cigaba da ƙoƙarin kamo sauran mutane da suka tsere.
John Onoja kwamandan jami’an tsaron yaƙi da hakar ma’adanai bi bisa ka’ida ya ce an kaddamar da bincike domin gano gurbatattun jami’an tsaron ya ƙara da cewa tuni aka rufe wurin biyo bayan samamen da suka kai.