An kaddamar da sabon kwaroron roba don sojoji

Rundunar sojin kasar Uganda ta kaddamar da wani sabon kwaroron roba wanda aka yi wa lakabi da “kariya” a harshen Swahili don kare sojojin kasar daga kamuwa da cutar kanjamau.

Soja ba zai iya kare kasarsa ba “idan shi ba ya cikin koshin lafiya”, in ji Shugaban Ma’aikata kasar Birgediya Leopold Kyanda lokacin bikin kaddamar da kwaroron roban.

Kimanin kashi 6 cikin 100 na mutane da suka wuce shekara 18 ne ke fama da cutar kanjamau a kasar.

Sai dai ana ci gaba da samun nasara wajen yaki da bazuwar cutar.

A baya, rundunar sojin kasar ce ta fi yawan sabbin mutanen da ke harbuwa da cutar.

Sabon kwaroron robar mai suna, Ulinzi, mai launin kakin soji zai taimaka wajen kiyaye bazuwar cutar a kasar, kamar yadda Ministan Lafiya kasar Vastha Kibirige ta bayyana.

“Aikin soja yana tattare da kalubale. Sojoji suna zuwa fagen daga inda suke saduwa da wadansu mata a can.”

“Yana da kyau su yi amfani da wata kariya don kada su kawo wa matansu da ke gida cututtuka,” in ji ta.

Kimanin mutane fiye da miliyan ne suke fama da cutar kanjamau a kasar Uganda.

More from this stream

Recomended