A daren ranar litinin ne aka bayar da rahoton jin harbin bindiga a kusa da karamar fadar inda hambararren Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ke zama a Nasarawa GRA na babban birnin jihar.
Fadar tana da nisan mita 300 zuwa gidan gwamnatin Kano inda aka takaita zirga-zirgar ababen hawa zuwa kashi daya na titin da ke kaiwa Tarauni.
Wannan dai ba zai rasa nasaba da dambarwar sarauta da ake fama da ita a Kano ba.