An haramta gangamin taron murna a Sokoto kan hukuncin shari’ar zaɓen gwamnan jihar

Rundunar yan sandan jihar Sokoto ta haramta duk wani gangami ko jerin gwano gabanin ko kuma bayan sanar da hukuncin shari’ar zaɓen gwamnan jihar da za ayi a ranar Asabar.

Kwamishinan yan sandan jihar Sokoto , Ali Kaigama shi ne ya fadi haka cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Ahmad Rufa’i ya fitar a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce rundunar ta samu bayanan cewa wasu sun kuduri aniyar yin jerin gwano ko kuma nuna murna ga hukuncin kotun.

Kasancewar jihar Sokoto jiha ce da aka santa da zaman lafiya rundunar ta ce baza ta bari ayi wani taro ba da ta ya saba doka ko wanda zai kawo tashin hankali.

More News

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 32 a yankin Neja Delta

Dakarun sojan Najeriya na runduna ta 6 dake Fatakwal sun samu nasarar lalata haramtattun matatun man fetur 32 tare da ƙwace lita 250,000 na...

An gudanar da bikin cikar Kwankwaso shekara 68.

Tarin magoya baya da kuma abokanan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Kwankwaso ne suka halarci taron lakca da aka shirya domin bikin...

Faruk Lawan ya kammala zaman gidan yarin Kuje

An sako tsohon ɗan majalisar wakilai ta tarayya, Hon Faruk Lawan daga gidan yarin Kuje bayan da ya kammala zaman gidan yarin na shekaru...

Sojojin Najeriya Sun Musanta Jita-jitar Mutuwar Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja

Daga Sabiu AbdullahiRundunar Sojojin Najeriya ta karyata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja,...