An haramta amfani da Adaidaita Sahu daga 10:00 na dare a Kano

Gwamnatin jihar Kano ta dakatar amfani da babur ɗin Adaidaita sahu daga karfe 10:00pm zuwa 06:00 na safe.

Wata sanarwar da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar ta ce hanin zai fara aiki daga ranar Alhamis 21 ga watan Yuli.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne a karshen taron majalisar tsaro ta jihar da aka gudanar.

Garba ya ce an ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaro lafiya da dukiyoyin al’umma

More from this stream

Recomended