An hana gudanar da sana’ar POS a ofisoshin ƴan sanda

Babban Sifetan Ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin dakatar da gudanar da sana’ar POS dama duk wani nau’in hada-hadar biyan kuɗi ta banki a harabar ofisoshin ƴan sanda dake faɗin ƙasarnan.

Egbetokun ya ce hanin ya zama dole ganin yadda al’umma suke cigaba da kokawa kan yadda suke zargin ana amfani da POS wajen biyan kuɗi ta haramtacciyar hanya ga wasu jami’an tsaro.

Shugaban ƴan sandan wanda ya yi magana ta bakin mai magana da yawun rundunar, Olumiyiwa  Adejobi ya ce anyi hanin ne domin ƙoƙarin kare mutunci  da kuma tsaron jami’an tsaro.

Ya jaddada cewa umarnin hanin zai kawar da zargin cin hanci da rashawa haka kuma zai hana ɓata gari  fakewa su shiga wuraren da sunan  cirar kudi da kuma ta tabbatar da oda a rundunar.

Babban jami’in ƴan sandan ya ce duk ofishin rundunar da aka samu ta saɓa umarnin to za a hukunta su tare da masu yin POS ɗin.

More from this stream

Recomended