‘
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun gwabza kazamin fada da mayakan Boko Haram a ranar Laraba, lokacin da ‘yan ta-da-kayar-bayan suka yi yunkurin kutsa wa garin Gashigar a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Mai magana da yawun rundunar Janar Texas Chukwu ya ce ‘yan ta-da-kayar-bayan sun je ne cikin manyan motoci guda tara, ‘ko da yake sun gamu da gamonsu a hannun dakarun kasar, inda suka yi musu fata-fata tare da haifar musu da asara ta mutane da kayan aiki.’
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce a yanzu haka dakarun sojin kasar sun mamaye yankin Gashigar da kewaye inda suke yin sunturi bayan faruwar lamarin.
Ta kuma bukaci da al’ummar yankin su kwantar da hankali tare da tabbatar musu da cewa suna cikin tsaro.A lokaci guda ita ma kungiyar IS a Afirka Ta Yamma ISWA, ta yi ikirarin kashe sojojin Najeriya bakwai tare da jikkata wasu a wani harin kwanton bauna ranar Larabar a garin Abadam.
Boko Haram a takaice
- An kafa ta a shekarar 2002
- Sunanta da Larabci shi ne, Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad
- Ta fara aikinta ne da nuna kin jinin karatun boko
- Ta kaddamar da kai hare-hare a shekarar 2009 da zummar samar da daular musulunci
- Amurka ta ayyana ta a matsayin kungiyar ta’adda a 2013
- Kungiyar ta ayyana wasu yankuna da ta kame a matsayin daulolin musulunci a shekarar 2014
- A yanzu haka sojoji sun kwato mafi yawan yankunan
- An samu rabuwar kai a shugabancin kungiyar tsakanin bangaren Shekau da na Al-Barnawi.