Zagazola Makama wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma kwararre kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi, ya bayyana cewa ya samu wasika daga kungiyar ISWAP da ke kalubalantar kungiyar Boko Haram wacce ta taɓa zama karkashin jagorancin Abubakar Shekau da yin fada da juna.
A cewar Zagazola, ISWAP ta zargi kungiyar ta Boko Haram da yaudarar jama’a, yada labaran karya, boye bayanai, cin hanci da rashawa, da fyade da ake yi wa mata da sunan bautar Allah.
A ranar Juma’ar da ta gabata, ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aike ta shafinsa na sada zumunta, inda ya ce tuni kungiyar Boko Haram ta karbi goron gayyatar.
Ya ce fadan da aka yi a Gaizuwa ya yi sanadin asarar rayuka da dama daga bangarorin biyu.
Masanin tsaro ya fitar da wata sanarwa ta daban a jiya Laraba yana mai cewa mayakan Boko Haram sun kama mayakan ISWAP 60 da suka hada da wasu muhimman kwamandojin kungiyar guda uku.
An tsare kwamandojin na ISWAP a jihar Borno, kamar yadda Zagozola ya bayyana, wanda ya bayyana sunayensu kamar haka: Abubakar Saddiq, Abou Maimuna, da kuma Malam Idris.