An gudanar da zanga-zangar adawa da rushe gine-gine a Kano

Daruruwan masu zanga-zanga sun bazama kan titunan jihar Kano inda suke nuna adawa kan rushe gine-gine da gwamnatin jihar ta ke yi.

Gwamnatin jihar Kano ta rushe gine-gine da dama a yayin da aka yi wa wasu alamar za a rushe su a nan gaba.

A cewar gwamnatin an dauki matakin ne saboda gwamnatin da ta gabata ta bayar da filayen gine-ginen ba bisa ka’ida ba.

Masu zanga-zangar na dauke da kwalayen da aka rubuta “Gwamna Yusuf abin da kake na korar masu zuba jari,” da sauran kalamai iri-iri.

Masu zanga-zanga sun taru ne otal din Daula da aka rushe inda suka wuce zuwa hedikwatar hukumar yan sanda ta jihar Kano domin su mika kokensu a hukumance.

More from this stream

Recomended