An gudanar da jana’izar tsohon shugaban majalisar wakilai ta tarayya Hon. Ghali Umar Na’Abba a fadar filin kofar kudu dake fadar qmai martaba sarkin Kano.
Dubban mutane da suka hada da jiga-jigan yan siyasa dama masoya da yan uwa suka halarci sallar Jana’izar marigayin.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima na daya daga cikin manyan yan siyasar da suka samu damar halartar sallar Jana’izar.
Marigayin ya mutu ne a wani asibiti dake Abuja bayan gajeruwar jinya.