A gano gawar wani mataimakin Sifiritandan Ƴan sanda Musa Yakubu dake aiki da ofishin ƴan sanda na Yaba a karamar hukumar Abaji dake birnin tarayya Abuja..
Wata majiyar ƴan sanda da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust cewa marigayin ya mutu ne a ranar Laraba bayan da ya tashi daga wurin aiki.
Ya ce marigayin na cikin koshin lafiya da walwala har ya zuwa ranar Laraba lokacin da aka gano gawarsa a cikin ɗakin baccinsa.
” A taƙaice muna tare da shi a ofis har kusan tsakar dare ranar Talata amma da safiyar ranar Laraba sai ba mu ganshi a ofis ba sai muka tafi ɗakinsa kawai sai muka samu gawarsa a cikin ɗakin,”
Marigayin da asalin garin Gwargwada ne dake ƙaramar hukumar Kuje dake birnin kuma na daga cikin ƴan sandan da aka yi wa ƙarin girma ya zuwa Mukaddashin Sifiritandan Ƴan sanda kwanan nan.