An gano gawar wani ɗan sanda da aka yi garkuwa da shi a jihar Filato

An gano gawar wani ɗan sandan kwantar da tarzoma da aka yi garkuwa da shi a wajejen garin Kampani dake gundumar Bashar a ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.

Ɗan sandan tare da wani jami’in soja na daga cikin tawagar jami’an tsaro dake yaƙi da ƴan fashin daji dake addabar al’ummar yankin da ya yi iyaka da jihar Taraba na kuma ɗauke su ne a  wani harin kwanton ɓauna da aka kai musu.

Sojan ya samu nasarar tserewa ayayin da  ɗan sandan ya gaza samun sa’ar yin haka.

Wasu majiyoyi dake garin na Wase sun bayyana cewa an gano gawar dan sandan ne a ƙauyen Bangalala a ranar Lahadi.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, DSP Alfred Alabo bai ce komai ba akan batun duk da tuntubar shi da manema labarai suka yi.

More from this stream

Recomended