An gano babbar mahadar bam ta yan kungiyar IPOB a Ebonyi

Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta gano wasu abubuwan fashewaa wani wuri mallakin kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra.

Sanarwar ta ce maboyar da aka gano bama-baman nan ne wurin hada bam mafi girma a yankin kudu maso gabas da aka gano.

Yankin kudu maso gabas ya jima na fama da hare-hare musamman kan hukumomin gwamnati da kuma mutane musamman da suka fito daga yankin arewa.

More from this stream

Recomended