An gama kada kuri’a a babban zaben Afirka ta Kudu

Shugaba Cyril Ramaphosa

Hakkin mallakar hoto
MICHELE SPATARI

Image caption

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu

‘Yan Afirka ta Kudu sun fito kwansu da kwarkwatarsu daga birane zuwa kauyuka domin zaben wadanda za su jagorance su nan da shekaru biyar masu zuwa.

A lokacin da ya kada kuri’arsa, Shugaba Cyril Ramaphosa ya bai wa ‘yan kasar hakuri saboda abin da ya kira ‘kuskuren da jam’iyyarsa ta ANC ta yi a shekarun da ta shafe tana mulkin kasar.

Amma shugaban ya ce yana da karfin gwuiwa cewa jamiiyyar tasa za ta sami nasara kuma yayi alkawarin kawo sauyi mai ma’ana da zarar hakan ya samu.

Masu nazarin harkokin siyasar kasar na ganin wannan zaben zai kasance wanda ya fi jan hankulan ‘yan kasar, kuma za a fafata sosai tsakanin manyan jam’iyyun siyasa na kasar.

Hakkin mallakar hoto
Reuters

Image caption

Masu kada kuri’a sun tsaya kan layi har dare a wasu yankunan kasar

Mutane da dama sun ce za su mara wa jam’iyyar ANC mai mulkin kasar baya… inda suke fatan Shugaba Cyril Ramaphosa zai kawo karshen shekaru goma na koma bayan tattalin arziki da rashin iya mulki a kasar.

A yayin da ya ke kada tasa kuri’ar a wata rumfar zabe, Mista Ramaphosa ya ba al’umomin kasar hakuri kan abin da ya kira matsalar cin hanci da rashawar da suka ki ci, suka ki cinyewa.

Jagoran jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance, Mmusi Maimane ya yi kira ga jama’ar kasar da su mara wa jam’iyyarsa baya, kuma su kawo sauyi na siyasa mai ma’ana a kasar.

Duk da cewa ANC ce ake sa ran za ta lashe zaben a matakin tarayya, amma za ta sha kaye a wasu larduna na kasar masu muhimmanci matuka.

Ita ma jam’iyyar Economic Freedom Fighters, EFF za ta kara karfi, kuma za ta iya zama wata muhimmiyar jam’iyyar siyasa a kasar.

More from this stream

Recomended