Hukumar kula da gidajen gyaran Hali ta Najeriya ta fitar jerin wasu hotuna na mutane 69 da ta bayyana da yan taaddar Boko Haram da suka tsere daga gidan yarin Kuje.
Hukumar ta bayyana haka ne cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Intanet.
Sakon mai dauke da hotunan yan ta’addar ya nemi jama’a su taimaka wajen bayar da bayanan da za su kai ga kama su.