An dakatar da sarkin da ya naɗa dan ta’adda Sarauta a Zamfara

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da Sarkin Birnin Yandoto a karamar hukumar Tsafe ta jihar,Alhaji Aliyu Marafa bayan da ya naɗa wani kasurgumin dan bindiga, Ado Aleiro sarauta.

An naɗa Aleiro sarautar Sarkin Fulani a ranar Asabar.

A cewar sarkin an naɗa, Aleiro sarautar ne sakamakon rawar da ya taka wajen sulhun zaman lafiya tsakanin masarautar da kuma yan bindigar da suke addabar karamar hukumar Tsafe.

Amma kuma a wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe Sardauna ya fitar gwamnatin ta nesanta kanta daga nadin sarautar da aka yi inda ta sanar da dakatarwar da gaggawa.

Tuni dai aka naɗa hakimin Yandoto, Alhaji Mahe Marafa domin ya cigaba da jagorantar masarautar.

More News

An kori sojojin da suka kashe wani jami’in NDLEA a Neja

Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar tare da korar wasu sojoji shida da ake zargi da hannu a mutuwar wani jami’in hukumar NDLEA, Kingsley Chimetalo,...

Maniyyayan Najeriya sama da 18,000 sun isa Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce adadin maniyyata 18,906 na shekarar 2024/1445 aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudiyya.Hukumar ta bayyana hakan ne a rana...

Talauci ko rashin wadata ba dalili ne na ƙazanta ba

Daga Aliyu M. AhmadBa tilas sai ka sanya manyan shadda ko yadi ba, ka ɗinka daidai da kai, kilaritarka ta sha gugar charcoal. Sutura...

Ƴan sanda sun kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a Kaduna

Jami'an ƴan sanda sun samu nasarar kama wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane a jihar Kaduna. Mutumin da aka kama mai suna, Muhammad Bello ɗan...