An dage ranar gudanar da zaben kananan hukumomin jihar Ribas

Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ribas(RSIEC) ta sanar da ranar 30 ga watan Agusta a matsayin sabuwar ranar da za a gudanar da zaben kananan hukumomin jihar.

Tun da farko an shirya gudanar da zaben kananan hukumomin ranar 9 ga watan Augusta amma yanzu aka daga shi zuwa ranar 30 ga wata a cewar hukumar zabe ta jihar sakamakon dokar ta baci da aka saka a jihar.

A cikin watan Faburairu ne kotun koli ta soke zaben da aka gudanar a jihar a shekarar 2024 inda ta kori dukkanin shugabannin da aka zaba ta hanyar zaben.

Shugaban hukumar zaben ta RSIEC, Michael Odey shi ne ya sanar dage zaben da aka yi a lokacin taron masu ruwa da tsaki kan zaben.

More from this stream

Recomended