An ceto wani mutum daga cikin baraguzan ginin bene bayan ya shafe sa’o’i 10

Masu aikin ceto sun samu nasarar ceto, Aliyu Salisu wani dan kasar Jamhuriyar Nijar daga cikin baraguzan ginin bene mai hawa uku da ya ruguzo bayan da ya shafe sama da sa’o’i 10 a cikin baraguzan.

A wata sanarwa da aka fitar ranar Lahadi, Josephine Adeh mai magana da yawun yan sandan birnin ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:15 na yammacin ranar Asabar a unguwar Life Camp dake birnin na Abuja.

Adeh ta ce yan sanda sun sun samu kiran kai daukin gaggawa inda suka gaggauta tattara tawagar masu aikin ceto suka nufi wurin isar su ke da wuya su ka killace wurin ta re da fara aiki ka’in da na’in.

Aikin ceto ya hada da jami’an hukumar bada agajin gaggawa ta kasa, NEMA na sashen kula da gine-gine na hukumar birnin tarayya Abuja FCTA da sauran jami’an tsaro dake aikin sintiri.

Adeh ta ce jami’an aikin ceto sun samu nasarar ceto Salisu da karfe 04:00 na asubahin ranar Lahadi.

“An gaggauta kai shi asibitin Cedar Crest dake Gudu inda yanzu yake samun kulawar likitoci, ” a cewar sanarwar.

More from this stream

Recomended