An Ceto Dalibai Da Ma’aikatan Makarantar St. Mary’s, An Kuma Hada Su Da Iyayensu A Jihar Niger

Diocese na Katolika na Kontagora ya tabbatar da cewa an samu nasarar ceto dukkan dalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary’s Catholic Schools da aka sace a Papiri, Jihar Niger, tare da mayar da su hannun iyayensu lafiya.

Mai kula da makarantar, Rev. Bulus Yohanna, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis. Ya ce mutane 230 ne aka tabbatar an sace su, wadanda suka hada da ma’aikata 12, dalibai 14 da kuma kananan yara 204.

Ya kara da cewa bayan kammala bincike da tantancewa, an tabbatar da cewa babu wani yaro da har yanzu yake bace. Rev. Yohanna ya ce an samu rudani a farkon tantancewar sakamakon yanayin firgici da tashin hankali da ya biyo bayan harin, inda wasu yara suka tsere zuwa dazuzzuka, yayin da wasu iyaye ba su halarci tantancewar farko ba.

Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Niger da jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi wajen ceto wadanda aka sace. Haka kuma ya gode wa iyaye, al’ummar Kirista, kafafen yada labarai da jama’a baki daya bisa addu’o’i, hakuri da goyon bayan da suka bayar.

Ya kuma yi addu’a domin samun waraka da farfadowa ga dukkan iyalan da abin ya shafa.

More from this stream

Recomended