An ba wa sojoji tukwici saboda ƙin karɓar cin hanci daga wasu ɓarayin shanu

Rundunar soji ta musamman mai kula da wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta bayyana cewa, a ranar Talata, ta bayar da tukwici ga wasu jami’an ‘Operation Safe Haven’ guda takwas bisa kin karbar cin hancin N1.5m daga wasu da ake zargin barayin shanu ne a jihar.

Kakakin rundunar, Kaftin Oya James, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce jami’an 8 da aka tura a sashin OPSH 4, sun kama wasu barayin shanu 30 a shingen binciken Bisichi da ke karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar.

A cewarsa, an yi awon gaba da shanun wani Shehu Umar ne a garin Mangu kuma ana ƙoƙarin kai su zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.

Har sai da dakarun rundunar da ke aikin kawo lumana suka tare su.

More from this stream

Recomended