An ɗaure matashi wata 6 a gidan yari saboda satar wasu kayayyakin cikin gida

Rundunar jami’an farin kaya ta Najeriya reshen jihar Ogun ta kama wani Kolajo Damilare da laifin satar kayan gida na wani Razaq Salaudeen a yankin Abeokuta na jihar na tsawon watanni shida a gidan yari.

Kwamandan NSCDC na jihar, David Ojelabi, ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho ranar Lahadi.

A cewar Ojelabi, jami’an NSCDC da ke Opeji Dibision ne suka kama wanda ake tuhuma a ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023, da misalin karfe 11 na safe, a yayin da yake aikin sintiri a yankin Bode Olude.

Ya kara da cewa Damilare ya amsa laifin satar kayan gidan da suka hada da firji, stabilizer da fitilar tsaro mallakar Salaudeen bayan an yi masa tambayoyi.

More News

Kotu ta sauke kakakin majalisar Nasarawa

Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta kori kakakin majalisar dokokin jihar Nasarawa, Rt. Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi dan jam’iyyar...

Masu cin gajiyar shirin Npower na kokawa game da rashin biyansu

Wasu masu cin gajiyar shirin gwamnatin tarayya na N-Power a ranar Litinin sun koka kan yadda ake ci gaba da biyan su alawus-alawus din...

Tinubu ya sake naɗa Mele Kyari a matsayin shugaban NNPCL

Shugaba Bola Tinubu ya sake nada Malam Mele Kyari a matsayin babban jami’in gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL). An bayyana hakan ne...

Ba baƙon abu ba ne don an haifi yaro da haƙori a bakinsa—in ji masana lafiyar yara

Likitocin kula da lafiyar yara sun ce jariran da ke da hakora daya ko biyu a lokacin haihuwa hakan ba baƙon al'amari ba ne. Wannan...