A yau Litinin ne matatar mai ta Dangote ta fara aiki.
An kera matatar man ne don fitar da ganga 650,000 a kowacce rana domin sarrafa ma’aunin danyen mai daga nahiyoyi uku na Afirka, Asiya da Amurka.
An kuma tattaro cewa matatar ta za ta kai rarar lita miliyan 38 na man fetur, dizal, kananzir da kuma man jiragen sama a kowace rana ga Najeriya.
Don haka za ta cika kaso 100 na man da kasar ke bukata.
Bayanai sun nuna cewa matatar ta Dangote za ta iya tallafawa wajen kafa gidajen mai guda 26,716, da samar da ayyukan yi na kai tsaye 100,000, da kuma samar da kasuwar danyen mai ta Najeriya $21bn a duk shekara.
