Amitabh Bachchan ya ba da tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa

[ad_1]

Amita Bachchan

Hakkin mallakar hoto
The Indian Express

A karshen watan Yulin da ya gabata ne jihar Kerala da ke kasar Indiya ta fuskanci mamakon ruwan sama, lamarin da ya haifar da mummunar ambaliyar ruwan da ka shafe shekaru ba a samu irinta ba.

Ambaliyar ruwan ta sanya mutanen da ke sassan jihar shiga mawuyacin yanayi na rashin matsugunnai da kuma sauran abubuwan more rayuwa.

Ambaliyar ruwan ta janyo mutuwar mutane fiye da 300, yayin da wasu da dama kuma suka samu raunuka baya ga rasa muhallansu.

Al’ummar jihar da dama sun shiga halin ha’ula’i, lamarin da ya sa suke bukatar agajin gaggawa.

Gwamnatin kasar Indiya tare da taimakon wasu kasashen duniya sun bayar da muhimmiyar gudunmuwa ga miliyoyin mutanen da wannan ambaliya ta shafa.

Su ma jaruman kasar, ba a bar su a baya ba, wajen bayar da ta su ga gudunmuwar ga mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa.

Jarumi Amitabh Bachchan tare da iyalansa, su jajanta tare da bayar da gudunmuwar zunzurutun kudi har 51 Lakhs, kwatankwacin dalar Amurka fiye da miliyan shida.

Hakkin mallakar hoto
GQ India

Shahrukh Khan ma ba a bar shi a baya ba wajen bayar da ta sa gudunmuwar ga mutanen, inda gidauniyarsa ta Meer ta bayar da 21 Lakhs, kwatankwacin dala miliyan biyu.

Sai kuma Akshay Kumar, wanda shi ma ya bayar da 25 Lakhs, kwatankwacin dala miliyan uku.

Jarumai mata ma ba a bar su a baya ba wajen bayar da gugunmuwa ga wadanda bala’in ambaliyar Kerala ta shafa, inda jaruma Jacquelin Fernandez ma ta bayar da Lakks biyar, wato kwatankwacin dubu dari shida.

Hakkin mallakar hoto
India Forums

Anushka Sharma da mijinta Virat Kohli, ma sun yunkura, domin sun bayar da ta su gudunmuwar.

Baya ga jaruman fina-finan kasar ta Indiya, daraktoci da masu shirya fina-finai ma sun ba da ta su gudunmuwar, kamar Priyadarshan da dai sauransu.

Jaruman da suka bayar da gudunmuwarsu, sun bukaci sauran takwarorinsu da kuma masu hannu da shuni da su ma su yunkura domin taimakawa wadanda annobar ambaliyar ruwan ta shafa.

Karanta wasu karin labaran

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...