Amirka ta musanta kai wa sojin Iran hari

Rouhani da Trump


Shugaba Rouhani da Trump sun samu sabani tun bayan janyewar Amirka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta 2015

Amurika ta nisanta kanta da zargin da shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi na cewa Washington da kawayenta na yankin gabas ta tsakiya na da hannu a harin da aka kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojoji da dama.

An dai kai harin ne a birnin Ahvaz kan sojojin kasar ta Iran.To sai dai tuni wasu kungiyoyi suka dauki alhakin kai harin.

Jakadan Amurika a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley ta sanar da cewa kamata ya yi shugaba Rouhani ya yi kyakkyawan nazari kafin ya dora alhakin harin kan Amurika.

Haley ta zargi shugaban na Iran da mai mulkin mulaka’u da ya bar al’ummar kasar shi cikin kangi na tsawon lokaci.

A na shi bangare, Anwar Gargash, wani minista na daya daga cikin kasashen yankin daular larabawa ya danganta kalaman na Tehran a matsayin wadanda basu da tushe barae makama.

Wata kabila daga cikin kabilun larabawa ‘yan aware da kuma kungiyar musulmi masu fafutuka da makamai ,dsu ne suka dauki alhakin kai harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 25.

Reshen kungiyar musulmi masu fafutuka da makamai wato IS mai kulla da farfaganda wato AMAQ ta nuna bidiyon wasu mutane 3 a cikin mota da sukai ikirarin su ne suka kai harin, bidiyon ya nuna suna kan hanyar zuwa birnin Ahvaz inda suka aika barnar.

More from this stream

Recomended