Akalla mutane uku ne ambaliyar ruwa ta tafi da su sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da aka samu a garin Zariya, jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa an gano gawar mutum ɗaya, yayin da wasu da dama har yanzu ba a gansu ba.
Wani shaida mai suna Mustapha Badamasi, wanda aka fi sani da Dan Bakano na Tudun Jukun, ya bayyana cewa an gano gawar Yusuf Surajo, da ake kira Abba. Ya ce wadanda har yanzu ba a gansu ba sun haɗa da Fatima Sani Danmarke da ɗanta mai shekara uku, da kuma wani mai babur.
Badamasi ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a kan babban titin Gaskiya kusa da wani coci a Tudun Jukun, lokacin da ruwan sama ya cika wata babbar magudanar ruwa a gefen hanya.
A cewarsa, mai babur ɗin na ɗauke da matar da ɗanta ne lokacin da babur ɗin ya bugi gefen magudanar. Ya ce matar ta zame a ƙoƙarinta na tsallaka magudanar a ƙafa, inda ta faɗa cikin ruwa tare da jaririnta. Ruwan ya yi awon gaba da su gaba ɗaya, ciki har da mai babur.
“Wani mutum mai ƙwazo da ya yi yunƙurin ceto su ma ruwan ya tafi da shi,” in ji Badamasi.
Imam Malam Musa Umar Al-Mishawi, wanda ya jagoranci sallar jana’izar Surajo a Kwarin Dangoma, ya tabbatar da cewa mamacin ya samu rauni a kai kafin ya riga mu gidan gaskiya. An binne shi bisa tsarin Musulunci.
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Ajalin Mahaifiya Da Ɗanta A Zariya
