Garin Hong, hedkwatar karamar hukumar Hong a Jihar Adamawa, ya gamu da ambaliyar ruwa mai tsanani a ranar Laraba, lamarin da ya jefa al’umma cikin tashin hankali.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa ruwan sama mai yawa da aka tafka ya haddasa ambaliyar, inda koguna da magudanan ruwa suka yi cike suka kuma zube.
Wannan shi ne karo na uku cikin kasa da makonni uku da aka samu ambaliyar ruwa a jihar Adamawa, bayan wanda ya faru a birnin Yola a ranar 27 ga Yuli. Haka kuma, shi ne karo na biyu a cikin mako guda a karamar hukumar Hong, bayan ambaliyar da ta auku a yankin Dugwaba a ranar 6 ga watan Agusta.
Rahotanni sun nuna cewa ambaliyar ta mamaye gidaje, gonaki da wasu muhimman kadarori, tare da tilasta daruruwan mazauna garin barin gidajensu da kasuwancinsu.
Sai dai, zuwa yammacin ranar Laraba, babu rahoton mutuwar wani a sakamakon ambaliyar.
Ambaliyar Ruwa Ta Mamaye Garin Hong a Jihar Adamawa
