Ambaliya ta lalata dukiyoyi da gidaje a Nasarawa

A kalla gidaje 60 da kadarori na miliyoyin naira sun lalace a jihar Nasarawa sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku a wasu kananan hukumomi biyu na jihar.

Babban Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar, Zachary Allumaga, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Lafiya a ranar Asabar.

Ya yi bayanin cewa ambaliyar ruwa da ta afku a kananan hukumomin Lafia da Toto a watan Agustan 2023, ta sa mazauna yankin da dama sun rasa matsuguni yayin da aka lalata wasu kayayyaki na wadanda abin ya shafa.

A cewar DG, ambaliyar ruwa da ta afku a garin Lafia ta shafi unguwar da dalibai ke zaune (Off-campus) a Jami’ar Tarayya ta Lafia tare da lalata kadarori irin su kwamfutoci, katifu, littattafai, kayan abinci da sauran kayayyaki masu daraja.

Yayin da yake karin bayani, Allumaga ya ce an sake samun wata ambaliyar ruwa a karamar hukumar Toto inda gidaje kusan 60 suka nutse tare da lalata kadarori da dama.

Shugaban Hukumar NASEMA wanda ya bayyana cewa ambaliyar ruwan a karamar hukumar Toto ta biyo bayan zaizayar da aka yi a yankin, ya kara da cewa an yi shirye-shiryen samar da kayan agaji ga al’ummar da abin ya shafa, da kuma Jami’ar Tarayya da ke Lafia.

More News

Ƴansanda sun hallaka masu garkuwa da mutane

Ƴansanda sun hallaka wasu masu garkuwa da mutane uku da ake zargin sun yi yunkurin yin garkuwa da matar wani dan majalisar dokokin jihar...

Ƴansanda a Katsina sun yi nasarar cafke wasu tantiran masu safarar alburusai wa ƴanbindiga

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Juma’a ta sanar da cewa ta kama wasu manyan ‘yan bindiga guda uku tare da kwato manyan...

Tinubu ya amince da mafi karancin albashi na N70,000

Shugaba Bola Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma’aikatan Najeriya, inda ya yi alkawarin sake duba dokar mafi karancin...

Mutanen Isra’ila sama da rabin miliyan sun tsere saboda yakin Gaza

Mutanen Isra'ila sama da rabin miliyan ɗaya ne suka fice daga ƙasar kuma ba su koma ba a watanni shida na farkon yaƙin Isra'ila...