Amarya ta ‘kashe’ jaririn kishiyarta da tafasasshiyar miyar kubewa

[ad_1]

jigawa police

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri ya ce akwai rashin jituwa a tsakanin kishiyoyin

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa a arewacin Najeriya ta ce tana tsare da wata amarya wadda ta watsa wa uwargidanta tare da danta dan wata 10 tafasasshiyar miyar kubewa a jikinsu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, SP Abdu Jinjiri ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a garin Gantsa da ke karamar hukumar Buji ta jihar.

Sai dai ya ce jajririn ya mutu sanadiyyar abin da ya faru.

SP Jinjiri, ya ce akwai rashin jituwa a tsakanin kishiyoyin.

Amaryar wadda ba ta wuce shekara 20 da haihuwa ba tana dakin girki ne a lokacin da uwargidan, rungume da danta, ta shiga dakin dafa abincin, daga nan, sai amaryar ta fara mayar mata da magana.

Daga nan sai cacar baki ta kaure. Ba tare da ba ta lokaci ba ne kuma amaryar ta dauki tukunyar miya tana tafarfasa ta watsa wa uwargidan da danta a jikinsu.

Bayan ta watsa musu miyar ne amaryar kuma ta fara ihu tana neman a kawo musu dauki.

Mai magana da yawun yan sandan ya ce uwargidan tana babban asibitin Dutse tana karbar magani, kuma duk jikinta ya daye, amma yaron ya rasu.

Kwamshinan ‘yan sandan jihar Bala ya bayar da umarnin a kai amaryar da ta aikata lamarin sashen binciken kwakwaf domin gudanar da bincike da kuma yi mata hukuncin da ya dace.

BBC ta yi kokokarin jin ta bakin mijin matan wato Malam Hamza, amma wayarsa a rufe.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...