
Chibuike Rotimi Amaechi, tsohon gwamnan jihar Ribas kuma tsohon ministan sufuri a lokacin gwamnatin Buhari ya ce zai kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027 idan ya samu tikitin takarar jam’iyar ADC.
Amaechi ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin da yake wata tattaunawa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a baya.
A lokacin tattaunawar tsohon ministan ya ce tun da yake bai taba aikata magudin zabe ba inda ya ce a lokuta da dama yaki yarda ya karbi mukami na mamba a kwamitin zabe a jam’iyar APC.
“Ina fada ban taba tsayawa zabe tare da Tinubu ba. Nasan Tinubu sosai. Nasan karfinsa na kuma san rauninsa.Na san idan aka bani tikitin takara na jam’iyar ADC to tabbas zan kayar da shi,” ya ce .
“Na kalubalanci duk wani dan siyasa dake raye ko a mace da ya fito fili ya fadi cewa ina cikin masu magudin zabe”