Amaechi da Mai Mala sun ziyarci Abdullahi Adamu a gidansa dake Keffi

Tsohon shugaban jam’iyar APC na riko Mai Mala Buni da kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi sun ziyarci shugaban jam’iyar APC na kasa Abdullahi Adamu a gidansa dake birnin Keffi a jihar Nasarawa.

Babu wani bayani da aka rawaito mutanen uku sun tattauna ayayin ziyarar sai dai wasu na ganin ziyarar bata rasa nasaba da zaben 2023.

Akwai rade-radin da jama’a ke yadawa cewa Amaechi da Buni na takarar shugaban kasa da kuma mataimaki.

More from this stream

Recomended