Alakanta coronavirus da 5G “shirme ne’ | BBC Hausa

Wata mata da wayar hannu

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Masana kimiya a duniya sun yi Allawadai da zargin wata kullalliya da ake ikirarin cewa fasahar intanet ta 5G ta taimaka wajen yada cutar coronavirus.

An ta yada wani hoton bidiyo a kafofin sadarwa na intanet da ke nuna turakun sadarwa na wayoyi na ci da wuta a Birmingham da Merseyside, inda ake zargin kullalliya ce ta fasahar 5G.

An rarraba bidiyon a Facebook da YouTube da Istagram – ciki har da shafukan mutane masu dubban mabiya.

Amma masana kimiyya sun ce tunanin alakanta Covid 19 da 5G “shirme ne” kuma wanda ba zai taba yiwuwa ba.

Babban Daraktan hukumar lafiya ta Ingila, Stephen Powis ya bayyana wannan kutinguilar ta 5G a matsayin “labarin kanzon kurege mafi muni.”

Zargin kullalliya

Yawancin wadanda ke yada kullalliyar da ke ikirarin cewa 5G – tsarin Intanet mai karfi da wayoyin salula ke amfani da shi- shi ne dalilin cutar coronavirus.

An fara yada wannan kullalliyar ne a Facebook a karshen watan Janairu, lokacin da aka fara samun bullar cutar a Amurka.

Zarge-zargen sun kasu rukuni biyu:

  • Wani ya yi ikirarin cewa 5G na karya garkuwar jiki wanda zai kasance hanya mafi sauki da mutane za su kamu da cutar.
  • Dayan kuma ya yi zargin cewa ana iya yada cutar ta hanyar amfani da fasahar 5G.

Dukkanin wadannan tunanin “shirme ne,” a cewar Dr Simon Clarke, Farfasa a bangaren nazarin kwayoyin halittu a jami’ar Reading da ke Birtaniya.

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Turken sadarwa na wayoyin salula ya kama da wuta a Birmingham da Merseyside, wanda ya haifar da bincike

“Tunanin cewa 5G na karya garkuwar jiki bai ma cancanci a yi bincike ba,” inji Dr Clarke.

“Garkuwar jikinka na iya raguwa daga abubuwa da dama – ta hanyar gajiya wata rana, ko rashin cin abincin da ya dace. Wadannan ba su da girman da zai sa har ka kamu da cututtuka.”

“Duk da yake tururin da waya ke fitarwa mai karfi na iya haifar da zafi, amma 5G ba ya da karfin da zai zama illa ga mutane.”

Tururin da wayar salula ke fitarwa na iya shafar halittar jikinka yayin da zafinsu ya shafe ka, ma’ana garkuwar jikinka ba za ta yi aiki ba. Amma karfin tururin 5G kanana ne kuma ba su da karfin da za su yi illa ga garkuwar jiki. An yi nazari sosai kan wannan.”

Sakon maganadisu da ya shafi 5G da sauran fasahohi da suka shafi wayoyin salula ba su da karfin da za su lalata kwayoyin halitta – sabanin hasken rana wato Sun rays da kuma na hoton gabobi wato x-rays.

Adam Finn, Farfesa a fannin nazarin lafiyar yara da cuttukan da suka shafe su a Jami’ar Bristol ya kara da cewa abu ne mai wahala 5G ya yada cuta.

“Wannan annoba ta samo asali ne daga cutar da ke yaduwa daga wani da ya kamu zuwa wani. Mun san wannan gaskiya ne. Muna da cutar da muke bincike a dakin bincikenmu, da muka samu daga wani da ke dauke da ita. Cuta da kuma tururin maganadisu da ke aiki a wayoyin salula da intanet wani abu ne daban,” a cewarsa”

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Image caption

Intanet mai karfin 5G ya taimaka wajen binciken lafiyar masu coronavirus cikin sauri a China

Yana da muhimmanci a fahimci wani raunin da ke tattare da wannan kullalliyar ta 5G – coronavirus na yaduwa a biranen Birtaniya wadanda ba su amfani da 5G, da kuma kasashe kamar Iran wadanda ba su ma fara amfani da fasahar ba.

Akwai labarai da dama na ban tsoro game da 5G da ke yawo kafin barkewar cutar coronavirus, inda tuni cibiyar da ke bin diddigi ta Reality Check ta yi bincike akai, kamar wannan labarin: Ko 5G baranazana ne ga lafiya?

Tun a farkon wannan shekarar, wani babban binciken hukumar kare tururi ta Non-Ionizing Radiation Protection (ICNIRP) ta yi watsi da wannan ikirarin, tana cewa babu wasu hujjoji cewa amfani da wayar salula na haifar da cutar kansa ko wasu cututtuka.

Amma idan akwai wani bu, labarin karyar tuni ya bazu.

Cututtuka na mamaye mutane ko kwayoyin halitta kuma suna amfani da su don hayayyafa, wanda shi ke haifar da cuta. Cututtuka ba su dade wa sosai a wani abun da ba mai rai ba, dole su samu hanyar shiga – yawanci ta hanyar wani abu mai ruwa daga tari ko atishawa.

Kwayoyin halittar wannan coronavirus sun nuna suna yaduwa ne daga dabbobi zuwa dan Adam – sannan daga baya ta ci gaba da yaduwa daga mutum zuwa mutum.

Bibiyi Reality Check a Twitter

Related Articles