[ad_1]
Hakkin mallakar hoto
Facebook/EFCC
Ibrahim Magu ya ce za a hukunta maciya amana a cikin jami’an hukumar idan aka kama su
Shugaban hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, Ibrahim Magu, ya ce akwai wadanda ake zargin maciya amana ne cikin ma’aikatan hukumar wadanda ke fallasa ayyukan hukumar ga ‘yan siyasa.
Magu, wanda ya fadi hakan a wajen wani taro na masu ruwa da tsaki a harkar yaki da cin hanci da rashawa, ya ce, hukumar tana bincike game da ire-iren wadannan jami’an.
Ya kara da cewa da zarar an gano irin wadannan jami’an a hukumar, za a hukunta su.
Magu ya ce irin nasarorin da hukumar ta samu a kotu kan tsofaffin gwamnoni biyu ya nuna cewa hukumar tana taka rawar gani wajen yaki da cin hanci da rashawa.
- EFCC na zargin Gwamnan Benue da ‘wawure’ naira biliyan 22
- Kotu ta wanke tsohon Gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa
Shugaban hukumar ya ce irin wadannan nasarorin za su zama izina ga duk mai son halatta kudin haram a kasar.
Sai dai kuma tun ba yau ba wasu daga cikin ‘yan siyasa dake jam’iyyar hamayya ke ikirarin cewar EFCC tana nuna son kai wajen yakin da take yi da cin hanci da rashawa.
Kuma suna ikirarin cewar ba ta kama ‘yan jam’iyyar APC mai mulki.
Da aka yi masa tambaya game da wannan, sai shugaban hukumar ya ce babu ruwan EFCC da siyasa, kuma zargin ba zai hana hukumar yaki da cin hanci da rashawa ba.
[ad_2]