Akwai Bukatar Shugaba Buhari Ya Fadada Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa-Shani

[ad_1]

Alhaji Muhammad Shani, masanin tattalin arziki kuma tsohon ma’aikacin babban bankin Nigeria, yayi kira ga Shugaba Muhammad Buhari,da ya fadada aikin yaki da cin hanci da rashawa.

Alhaji Shani yaci gaba da cewa, ya kamata yaki da cin hanci da rashawa ya hada da batun daukan ma’aikata, da kwangila da ake bayarwa a ma’aikatu, da ma wasu batutuwan da suka shafi ‘yan Nigeria.

Alhaji Shani ya bayyana haka ne a wata hirar da ya yi da Sashen Hausa a birnin Maiduguri inda ya kara da cewa batun cin hanci da rashawa ya zama babbar annoba a kasar, kuma dole ne ‘yan Nigeria su ba da tasu gudummawar wajen taimakawa shugaban kasa.

Cin hanci da rashawa Mallam Shani yaci gaba da cewa, ta yiwa kasar katutu. Ya ce zai ba kansu laifi saboda bai kamata su ‘yan kasa su ce ba su san cewa lokacin da Buhari ya kama mulki cin hanci da rashawa ya riga ya zama ruwan dare gama duniya ba. A cewarsa aikin yana da yawa. Ya fi karfin mutum daya.

Cin hanci, injishi, har yanzu ana duba ta fuskar cin kudi ne kawai amma cin hanci da rashawa na daukan salo iri daban daban a Nigeria. Misali duk inda wani ya biya ma kansa buri ta hanyar da bata cancanta ba, ya ci hanci da rashawa.

Ya ce akwai cin hanci da rashawa wajen daukan ma’aikatan gwamnati, da har yanzu ba’a tabo shi ba. Akwai cin hanci da rashawa wajen daukan ma’aikata ko kara masu girma. Cin hanci da rashawa na iya haifar da illar rashin tsaro saboda wadanda ba’a daukesu aiki domin an fifita ‘ya’yan wasu fiye dasu suna iya sake hali.

Tsohon ma’aiakcin babban bankin, ya zargi babban bankin Nigeria da yin shiru akan wasu kudade kimanin dala biliyan 20 da tsohon gwamnan bankin ya ce sun bace. Maimakon gwamnan yanzu ya ci gaba da batun sai ya bari batun ya mutu. Haka ma batun baiwa manoman shinkafa kudi a jihar Borno, anan Mallam Shani yace an yi magudi.

Ga rahoton Haruna da karin bayani

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...