Akwai babbar barazana a Jihar Kano – AREWA News

A jiya tawagar SIRRINSU Media sun zanta da wasu mutane da suka shigo jihar Kano daga Legas wadanda jami’an Civil Defence suka kama. Sun tabbatar da cewar suna biyan kudi ne ga jami’an tsaro ana shigowa da su duk kuwa da babu tabbacin basu dauke da wannan cuta.

Sannan gidan Rediyon Rahma ya kawo Rahoton yadda likitoci ke ba wa masu cutar sakamakon su a hannu wai su kai kansu wajen killacewa ba tare da rakiyar jami’an lafiya ba. Ya Ilahu idan wani ya kai kansa wani zai kai?

Bugu da kari an yi hira da maigadin wajen killacewar ya ce yanzu haka ga masu cutar nan na jira a zo a dauke su babu motar da za a zo a dauke su. Wasu ma sun gaji sun tafi.

Wannan Rahoton akwai matukar razanarwa ya kamata Gwamnati ta ji shi ta kuma dauki matakin gaggawa.

More from this stream

Recomended