Akwai ƴan ƙasarmu kusan 200 da ke hannun Hamas—Isra’ila

A ranar Litinin ne sojojin Isra’ila suka ce adadin ƴan ƙassrsu da Hamas ta yi garkuwa da su sun karu zuwa 199 bayan harin da Hamas din ta kai.

Wani mai magana da yawun sojojin Isra’ila Daniel Hagari ne ya bayyana hakan cikin wata tattaunawa da kafofin yada labarai.

A baya dai Isra’ila ta saka adadin kan mutum 155 kafin yanzu da aka samu sauyin adadin.

Har yanzu dai ana ta gwabza faɗa tsakanin mayaƙan Hamas da Isra’ila.

More from this stream

Recomended