Akpabio ya bawa Natasha Akpoti hakuri

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bawa Sanata Natasha Akpoti daga jihar Kogi haƙuri kan furucin da ya yi mata akan gidan rawar disko a yayin wani zama na majalisar.

Akpabio yayin zaman majalisar a makon da ya gabata ya faÉ—awa sanata Akpoti cewa majalisar ba “gidan casu bane” dole ne a bawa mutum izini kafin ya yi magana biyo bayan magana da ta yi ba tare da izini ba.

Maganar da ya yi ta jawo suka daga Æ´an Najeriya da dama inda suke ganin tamkar ya ci zarafin sanatan ta hanyar danganta ta da rashin kamun kai.

A yayin zaman majalisar na ranar Talata da ya jagoranta, Akpabio ya bayar da haƙuri inda ya ce da saninsa ba zai wulakanta mace ba kuma ba yayi haka bane dan ya ci zarafin ta.

More News

NNPCL ya sake ƙarin kuɗin man fetur

Kamfanin mai na NNPCL ya sake ƙara kuɗin man fetur a gidajen mansa dake faɗin ƙasarnan. Wannan ne karo na biyu da kamfanin yake ƙara...

Tinubu ya bada umarnin gaggauta gyara wuta arewacin Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana damuwarsa kan matsalar rashin wutar lantarki da ake fama da ita a yankin arewacin Najeriya. Shugaban ƙasar ya...

Sojoji sun kama É“arayin É—anyen man fetur 35 a Neja Delta

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta sun kama mutane 35 da ake zarginsu da gudanar da haramtattun matatun man fetur da kuma lalata bututun...

Majalisar dokokin jihar Gombe ta zartar da dokar kafa hukumar kula da masu buƙata ta musamman

Majalisar dokokin jihar Gombe ta zartar da kudirin dokar da zai samar da hukumar  da za ta kula da da mutane masu buÆ™ata ta...